pacman, rainbows, and roller s
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na goma sha bakwai


Sayyed Zakzaky2

Ina matsayin sanya turare mai Alcohol a cikinsa?

TAMBAYA: Tarukan gwagwarmaya kamar ta'alimi da muzahara da mu'utamar. Shin hakkin miji ne sad da ya ga dama ya bar matarsa ta je ko kuwa duk sad da ta ji sanarwa tana iya halarta?

Daga Izzatu Sani Ruwan Sanyi Karfi Jihar Katsina.

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da za mu iya cewa shi ne, ayyuka na addini wanda ya zama wajibi 'yan al'umma gaba dayanta mazansu da matansu su tsaya da shi, wajibi ne ga kowannensu. Amma don maslaha, akwai bukatar fahimta tsakanin mata da miji a kan wadannan al'amura. Ba batun ta ce kawai da ta ji sanarwa sai ta kama hanya kawai ta tafi bane. Saboda haka akwai bukatar ya yi mata izini. In hatta hajjin wajibi, an ce akwai bukatar mace ta nemi izinin mijinta, sai dai in ya hana ta sai ta tafi abinta. Saboda haka a irin harkokin addini wanda in ka ga ya hana ta ne da nufin shi ba ya bukatar ta yi Harkar addini ne gaba daya. Yanzu zaBi ya ba ta kenan tsakanin ko dai ta yi Harkar addinin, ko kuma ya hana. To sai ta zaBi na zaBa kenan, ko ta bi zaBin hanin, sai ta daina Harka din, ko kuma ta ga Harkar ta fiye mata duniyarta da lahirarta ta yi ba da izininsa ba, ala barshi wannan kuma in ya yi kamari, to ko su sasanta tsakaninsu a tafi a haka nan da auren? Ko kuma ma ya kai ma sun rabu, tunda dai sun bambanta a ra'ayi. Wannan lalle ba muhalli ne da za a ce hakki ne da duk lokacin da ya ga dama ya ce ta yi, in ya ga dama kuma ya ce ta bari ba. In har ya zama haka nan zai zama yana iya ganin dama ya hana ta Harkar addini gaba daya, sai ya zama shi kenan ta daina yi din kenan a matsayin shi hakkinsa ne, alhali ba shi da wannan hakkin. Amma ba fa ina nufin yanzu ba hakkinsa ne kawai ba a bukatar maslaha, sai kawai da ta ji sanarwa sai ta kama hanya abinta ba. Ka ga in haka ne zaman aure ba zai yi dadi ba kenan. Wato duk ma'abocin hakki dai ana ba shi hakkinsa. Yana da hakki ita ma tana da hakki. Daya bai share daya ba.


TAMBAYA: Shin zai halasta mutum ya sayi abin hadaya a nan gida, kafin ya tafi aikin hajji, sannan ya yiwo waya a daidai lokacin da yake son a yanka masa abin hadayar, idan an sanar da shi sannan ya kwance harami ya yi aski?

Daga Ahmad A Ibrahim Potiskum jihar Yobe.

SHAIKH ZAKZAKY: To, lalle wannan ba zai taBa yiwuwa ba. A nassin Alkur'ani "hadyan baligal Ka'aba." In dai hadaya ce, to lalle sai a can a Makka ake yankawa, ba a yankawa a wani wuri. Amma idan layya ce wanda yake bai shafi aikin hajjinsa ba. Kamar misali in hadaya ba ta kama shi ba, kamar ya yi nau'in hajjin nan da ke ce masa 'Ifradi' wanda ba hadaya a kansa, kuma wani abu na yin fidaya bai hau kansa ba, to in layya ce ya samu ya bugo waya ya ce a yi masa layya a gida a ci naman, shi ma a ajiye masa in ya dawo ya samu. Layya kenan. Amma ba hadaya ba. Hadaya dole sai a Makka. Hatta ma idan hadaya ta kama shi bai sami yi a can ba saboda ko rashin kudi, misali, ko kuma ya yi wani laifin da aka lizimta masa yin fidya, to in ya dawo ya samu ya ba da kudi a je can a sayi rago a yanka masa a can. Amma bai samu a yanka ragon a nan ba bayan ya dawo gida. Lazim ne sai a can ake yi.

TAMBAYA: Shin akwai mikidarin shekarun da mace za ta kai ya zama ba wajibcin sanya hijabi a kanta saboda tsufa?

Daga Ahmad A Ibrahim Potiskum jihar Yobe.

SHAIKH ZAKAKY: Eh, haka ne, muna iya cewa akwai mikidarin shekaru. In ita ma'abuciyar haila ce, sai ya zamana har ta zama ma ba ta yin haila din, wanda galiba yakan sami mata in sun dan shekara wajen 40 da 'yan kai zuwa 50, musamman wadda ba ta haihuwa sam-sam, amma tana haila. Ba wadda ba ta haila sam-sam ba, wadda da ma tana haila amma sai kuma hailar ta dauke. Da kuma in ya kasance ba ta da sha'awar ta yi aure, to ta samu ta ajiye hijabinta, amma ba mai tabarruji ba, kada ta yi tabarruji da ado. Wato ko da ta tsufa ba a ce ta yi tabarruji da ado ba. Saboda haka mikidarin tsufar, shi ne in ta kai ma misalin ba ta haila, wato Ya'isa, "walla'i ya'isna minal mahidi..," a cikin Alkur'ani. Wato in ta kai mikidarin ta daina haila alhali da tana yi. Domin akwai wacce ba ta yi tun asali, to ba ita muke nufi ba. Wadda da can tana yi amma sai kuma ta kai mikidarin ta daina kuma ba ta da sha'awar ta yi aure, to ba laifi gare ta ta ajiye hijabi, amma kada ta yi tabarruji da ado. Kada ta caBa ado ta rinka bayyana jikinta.

TAMBAYA: Menene matsayin kiyasi a Musulunci?

Daga Ahmad A Ibrahim Potiskum Jihar Yobe

SHAIKH ZAKAKY: Batun kiyasi dai, sai mu ce akwai hanyoyin samun hukunce-hukunce na shari'a wanda ma'abota ijtihadi kan yi daga littafin Allah da sunnar Manzon Allah. In ba a samu a wannan ba ana koma wa ijima'i, in ba a samu a wannan ba ana koma wa akal. Amma akwai daga cikin sauran mazhabobi suna cewa suna kiyasi. Akwai bambanci tsakanin kiyasi da akal. Akal, shi hankalin mujtahidi zai sa a fahimtarsa. Shi kuwa mai kiyasi, yana kwatanta wani hukunci ne da wani hukunci ya fitar. To in da kuma wannan yakan zama akwai mishkila kenan, saboda Allah (T), hukunce-hukuncensa yana dora shi ne ba bisa hankalin mutane ba. Kamar yadda Imam Ja'afar Assadik ya gaya wa wani mai kiyasi, ya tambaye shi cewa salla da azumi wannene ya fi? Sai ya ce masa salla! Sai ya ce, to me ya sa Allah ya ce, mace in tana haila ta mayar da azumi, amma ba salla ba? Sai ya zama ba amsa. Sai ya ce, saboda haka kar ka kwatanta wani hukunci da wani. Hukunci dai bar shi kawai yadda Allah ya ce a yi masa, a yi. Wannan kuwa zai nuna ka ga shi kiyasi zai zama mishkila ne, domin za ka kwatanta wani hukunci ne da wani hukunci, alhali Allah(T) kuma ba da irin naka hankalin yake hukuncinsa ba. Saboda haka in dai ba ka sami abu a wadannan masadir na shari'a ba, to sai ka koma wa akal. Amma akal din ba na kowane irin mutum ba, akal din Mujtahidi. Sai dai in ka sami kanka a wani halin da ba ka san ijtihadin ba kuma ba za ka iya tambaya ba, to a nan kai ma sai ka yi amfani da naka hankalin, daga baya ka binciki ko ya matsayinsa yake, amma ba za ka kwatanta shi da wani hukunci ba, ka ce tunda a wuri ka za ka za ake yi, to ka za ma zai zama shi ne wannan, ka ce ya zama shi ne hukuncinka.

TAMBAYA: Ina matsayin cire 'yar wuya ko belu da ake yi ga jirajirai?

Daga Ahmad A Ibrahim Potiskum jihar Yobe

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai wannan ba shi da wani hukunci, ba a san shi ba a karatu, al'adun mutanen Hausa ne kawai. Bilhasali ma an yi tambaya a BBC, amsoshin takardunku din nan, aka ce su ba da bayanin cire belu, suka ce iyaka bincikensu ya nuna cewa a duk duniya, Hausawa kawai ke cire belu. Saboda haka lallai al'ada ce kawai ta mutane, ba a halicce mu da wata cuta mai suna belu ba ballantana a ce. Amma wani lokaci idan ya zo da ciwo aka je asibiti, in akwai bukata ta yiwu a ce a cire. Amma da ma ba ka'ida ne a cire ba. Kamar loBa, wadda akan yi kaciya, da ma shi an ce a yi ne. Amma ba a san belu ba.

TAMBAYA: Ina matsayin sanya turare mai Alcohol a cikinsa?

Daga Ahmad A Ibrahim Potiskum jihar Yobe

SHAIKH ZAKZAKY: Ina jin mun sha amsa tambayar nan. Domin su mutane sun kasa gane ma'anar AlCOHOL. Sun dauka Alcohol shi ne giya. To Alcohol ba giya bane, ana dai yin giya ne da shi. To kuma abin da ake yin giya da shi, ba shi ne giya ba, ba lalle ya zama shi ne giya ba. Kamar misali ana yin giya da dawa da gero, amma su dawa da geron ba giyoyi ne ba. Amma shi Alcohol wani irin sinadari ne (Liquid) wanda yake ana debo shi daga abubuwa masu tsarki, shi ma kansa yana da tsarki. Amma akan yi amfani da shi wajen sarrafa abin da akan sha ya bugar. To in aka yi amfani da shi aka sarrafa abu ya zama giya, to yanzu sunansa giya. Don haka ma masu cewa Alcohol, ba suna ce masa Alcohol ne ba, suna ce masa abin sha mai Alcohol¸wato 'Alcoholic Drink.' Ba yadda za a yi a ce mutum ya sha Acohol. In mutum ma zai iya shan sinadarin Alcohol tsurarsa, an ce ma zai iya karkatsa masa hanji nan take, saboda sinadari ne wanda ake amfani da shi wajen sarrafa turare da wadansu abubuwa daban-daban, don yana hada abubuwan da aka tatso su daga ciki daban-daban, su narke su zama abu guda. Saboda haka shi a kan kansa, ba shi ne giya ba. Amma in giya ce wannan wadda akan sha a bugu, to ba yadda za a yi a zuba ta a turare, bilhasali ma da yawanta ma har wari take yi. Shi kuwa wannan sinadarin, wani abu ne bai da kanshi bai da wari, sannan kuma in ka ajiye shi ka bude shi a kwalba, ka bude kwalbar, zai bi iska, za ka dawo ka tarar babu shi, ya tafi abin shi. Saboda ba shi ne a kashin kansa shi ne giya ba, ko da ka ga an sa shi a turare. Saboda haka ba komai don an sa shi a turare. Amma in aka yi amfani da aka sarrafa abinci zuwa giya wanda za a sha a bugu, to ya haramta a sha wannan.

TAMBAYA: Menene hukuncin wanda ya yi aiki don riya, daga baya ya gane kuskuren da ya yi, kuma ya tuba. Shin za a mayar masa da ladan aikinsa ko sai ya sake wani?

Daga Muhammad Sani Layin Bola Rigasa Kaduna

SHAIKH ZAKZAKY: To a hukuncin shari'a dai ba a ce mutum zai sake aiki ba. In dai ya yi aiki ya inganta a nazarin shari'a, to shi kenan, niyyarsa kuma tsakaninsa da Allah. Kodayake akwai fadin cewa ba zai nisanta ya zama aikin da mutum ya san cewa lallai bai yi don Allah ba, ya zama babu shi.

TAMBAYA: Menene hukuncin karBar lada wajen wankan gawa?

Daga Yusuf Abdullahi Darazo Unguwar Lukos jihar Bauci

SHAIKH ZAKZAKY: To, in dai aikin wanke gawar ne, to haramun ne ya karBi lada saboda shi wajibi ne na kifaya, wanda in wani musulmi ya yi, ya dauke masu wannan. Saboda haka shi da ya yi aikin wankan, ya dauke wa sauran al'ummar musulmi. Sai dai akwai wadansu ayyuka wadanda tana iya yiwuwa a karBi ladansu, kamar a ce ruwa, masalan, ko kuma wani wankin da ya fita daga cikin ka'ida na wajibi, kamar a ce ko za a shafa masa wadansu abubuwa ko za a yi masa tausa ko wani abu da ya fita daga haddin ka'idar wanka. Kodayake ana iya yi, amma ya zama kamar na ganin dama, kamar in an so a yi. Amma bai zama na wajibi ba, to in a kan wannan ne, babu laifi. In ba haka ba in dai ainihin ladan yin wanka na wajibi ne, to ba zai karBa ba kuma haramun ne ya karBa.

TAMBAYA: Bankunan yanzu sun doru ne a kan kudin ruwa. Ina hukuncin aiki a cikinsu?

Daga Nasiru Ladan Waziri Darazo Fed-Poly.Bauci

SHAIKH ZAKZAKY: To,mun sha amsa tambayoyi irin wannan. Banki tamkar mutum ne mai ba da bashi da ruwa. Idan mutum yana ba da bashi da ruwa, akwai ayyukan da za ka iya yi masa, ya kuma halatta, akwai wanda za ka yi masa bai kuma halatta ba. Misali in kai magini ne, ya nemi ka yi masa gini, ya halatta ka yi masa gini. In kai mai sa famfo ne, ka sa masa famfo. In mai sa lantarki ne, ka masa lantarki. Amma ka rubuta masa takardun bashin da tunatar da masu bashi din cewa lokacin biya fa ya yi, da zuwa kakkarBo har da ruwan, to sune suka haramta. Wato aikin da ya shafi ainihin wannan abin da ya haramta din ne ba za ka yi ba, ba za ka yi masa ba. Amma wanda ya halatta, za ka yi. Saboda haka banki yana da ayyuka wadanda suka halatta yana da wadanda ba su halatta ba. Saboda haka sai ya kiyaye. In aikinsa ya shafi na halas, to babu laifi da wannan.

TAMBAYA: Wani masallaci ne aka gina amma kafin a gina sai da aka rinka cire kudi daga cikin albashin ma'aikata, ko suna so ko ba sa so. To menene hukuncin yin salla a wannan masallacin?

Daga Salisu Tukur Gaiwa Jihar Katsina

SHAIKH ZAKZAKY: To, lallai ba komai, wurin da aka hana yin salla shi ne kasa din, idan ta kwace ce. Idan inda aka gina masallacin na wani talaka ne aka kwace ma, alhali ba ya so, to shi ba za a iya salla a ciki ba ko da wadanda suka tara kudin suka gina suna so ne suka ba da kudin. Saboda haka abin la'akari shi ne kasa din ba wai rufin ginin ba. Saboda haka in dai kasar ta halas ce, inda aka yi masallcin, to ya halasta a yi salla a wurin.

TAMBAYA: Akwai wani ruwa da yake digowa daga cikin AC, idan aka tari wannan ruwa don yin ibada, shin ya inganta?

Daga Salisu Tukur Gaiwa Jihar Katsina

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, ai ruwa ne ba wai wani abu ne na daban ba, da shi da ruwan sama kamar matsayinsu guda, tunda yake daga irin iska mai damshi ne da ya shiga, shi yake tattarawa. Saboda haka kusan hukuncinsu daya ne da ruwan sama.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Mutum ne yake karatu kuma "Inservice"wato yana karBar albashinsa. Shin ya halasta kuma ya karBi "Scholarship" domin da ma albashin ba isa yake ba wajen daukar nauyin kansa da kuma sayen kayan karatu?

Daga Mahfuz Muhammad ABU Zariya

SHAIKH ZAKZAKY: Irin wannan sai dai mu koma wa Urfi, idan da ma adatan mutum ko yana aiki yana iya karBar 'Scholarship', sai mu ce ya yi. Amma in a bisa urfi ana ganin bai halatta masa ya karBi 'Scholarship' ba, alhali yana karBar albashi, kuma ma ba zai yiwu a ba shi 'Scholarship' din ba matukar an san yana karBar albashi ne sai dai ma in ya jujjuya takardu ne, ya nuna shi ba mai karBar albashi ne ba sannan zai je ya karBi wancan, sai mu ce ka ga yana karBar lada biyu kenan a aiki guda. Ina jin wannan mai tambayar, ko shi ko waninsa ya yi mani irin wannan, amma da na ba shi amsa shigen irin wannan, sai wani ya nuna mani cewa lallai akwai wadansu Ma'aikatu, kamar na gwamnatin Tarayya wadanda suke ba da 'Scholarship' alhali sun san mutum yana aiki. Saboda haka a lokaci guda yana karBar albashinsa yana kuma karBar ladan 'Scholarship' kuma ba a ganin cewa ya yi laifi. Saboda haka in wannan ne ka ga babu damuwa. Amma in ta kai ma sai ya yi karya na nuna takardu na daban cewa shi ba ma'aikaci bane domin ya karBi duka biyun, kuma in an gano za a ga cewa ya yi laifi, har ma kila ana iya hukunta shi, to sai a ce bai kamata ya yi haka nan ba.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din